22 Nuwamba 2020 - 13:21
​Rouhani:Gwamnati Za Ta Tallafawa Mutane Kimani Miliyon 30 Saboda Dokar Zaman Gida Da Aka Kafa

Shugaban kasar Iran Dr Hassan Rouhani ya bayyana cewa gwamnatin kasar za ta bawa mutane kimani miliyon 30 tallafin kudade don sawwaka masu radadin zaman gida da rufe kasuwannin da ake yi saboda dakile yaduwar cutar korona a kasar zuwa karshen wannan shekara.

ABNA24 : Shugaban ya bayyana haka ne a yau Asabar a lokacinda yake halattar taron kwamitin yaki da cutar korona na kasa a nan Tehran.

A yau Asabar ce aka fara daukar matakan takaida haduwar mutane tare da rufe kasuwannin da masana’antu domin dakile yaduwar cutar korona a kasar.

Wannan matakin zai ci gaba har na tsawon makonni biyu, a lokacinda kwamatin yaki da cutar zai sake zama don ganin mataki na gaba da zai dauka.

A cikin yan makonnin da suka gabata dai yawan wadanda suke kamuwa da kuma wadanda suke rasa rayukansu sadaiyar cutar sun yi yawa sosai, wanda ya sanya kwamitin ya ga cewa dole ne a dauki matakin hana haduwar mutane na tsawon makonni biyu.

342/